Kano: Magatakardan Jami’ar Bayero Ya Kwanta Dama

 Hukumar jami’ar Bayero ta Kano, BUK, ta sanar da rasuwar rijistaran jami’ar, Jamil Ahmad Salim.

A cewar wata sanarwa mai dauke da sa hannun shugaban jami’ar, Sagir Abbas, marigayin ya rasu ne a safiyar yau Laraba a Kano bayan gajeruwar rashin lafiya.

Sanarwar ta ci gaba da cewa: ” Jami’ar Bayero ta Kano, cikin alhini, na sanar da rasuwar rijistaran ta Malam Jamilu Ahmad Salim.

“Malam Salim, wanda shi ne magatakardar Jami’ar tsawon shekaru hudu da suka gabata, mutum ne mai kwazo da kwazo da jajircewa, wanda ya bayar da gudunmawa sosai ga ci gaban jami’ar.

An yi Jana’izar marigayin da karfe 10:00 na safe jiya babban masallacin BUK da ke New Campus, Kano

Related posts

Leave a Comment