Gombe: ‘Yan Adawa Sun Garzaya Kotu Kalubalantar Nasarar Gwamna Inuwa

Rahoton dake shigo mana daga jihar Gombe na bayyana cewar ?an takarar za?en gwamnan jihar na jam’iyyun PDP da ADC Jibrin Barde da Nafi’u Bala, sun maka gwamnan jihar, Muhammad Inuwa Yahaya, a gaban kotun sauraren ?ararrakin za?e.

An ruwaito cewa Barde da Bala sun garzaya gaban kotun bayan bayyanar sakamakon za?en gwamnan jihar na shekarar 2023 wanda ya ba Gwamna mai ci Alhaji Inuwa Yahaya nasara.

A takardar ?arar da suka ya shigar a gaban kotun, wa?anda aka sanya a cikin ?arar sun ha?a da hukumar za?e mai zaman kanta ta ?asa (INEC), Inuwa Yahaya da jam’iyyar sa ta All Progressives Congress (APC).

Related posts

Leave a Comment