Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Gwamnatin tarayya ta hannu Ministan Kwadago da Ayyuka, Chris Ngige, sun yi ganawa da kungiyar malaman jami’o’i ta kasa wato ASUU, a ranar Litinin.
Kwanaki 56 kenan da ASUU ta shiga yajin aiki sakamakon abin da ta bayyana gazawar gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari wajen aiwatar da yarjejeniyar da suka kulla a baya game da yadda za a inganta harkokin karatun jami’a na kasar.
ASUU dai na ganin yajin aikin ne hanyar karshe da take bi domin tilasta wa gwamnatin tarayya biya mata bukatunta.
Yajin aikin malamai a Najeriya ya fi yin tasiri a kan dalibai wadanda ke tsintar kansu cikin damuwa, dalilin da ya sa wasu ke ganin ya kamata kungiyar ta sauya salon tunkarar rikicinta da gwamnatin kasar ba sai lallai ta hanyar yajin aiki ba.
Wasu bayanai sun nuna cewa kungiyar ta ASUU ta daka yajin aiki sau 15 tun bayan komawar Najeriya mulkin dimokuradiyya a 1999, lamarin da kan jefa harkokin karatu cikin mawuyacin hali.
