Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar da akwai yiwuwar yakin da ake fafatawa tsakanin Rasha da Ukraine zai tsawaita karancin man fetur din da ake fuskanta fiye da makwanni uku da suka wuce, alamu sun nuna yawancin kayayyakin da matata ke samarwa da ake shigowa dasu cikin Najeriya, daga sasannin da ake yakin zasu fuskanci jinkiri.
An tattaro a ranar Lahadi, cewa ‘yan kasuwan dake sayarwa Najeriya kayyayakin da ake samarwa daga man fetur zasu iya samun tsaiko, saboda raguwar da aka samu na jiragen Kamfanin man fetur na Najeriya (NNPC).
Kamfanin NNPC yana shigo da tataccen man fetur cikin Najeriya, daga ‘yan kwangila da ‘yan kasuwa ta hanyar tsarin saye da sayarwa kai tsaye.
Tabbattatun majiyoyi daga masu harkar mai da sauran ‘yan kasuwa sun bayyana a ranar Lahadi yadda Najeriya ta samu raguwa na kimanin jiragen 17 a DSDP din ta, saboda raguwar samar da man fetur.
Sun ce, hakan ka iya tsawaita karancin man fetur din da ake fama dashi a fadin kasar, sai dai idan an yi amfani da matakin rashin dakatar da gudanarwar bangarorin man fetur.
Sun kara da bayyana yadda yakin Rasha da Ukraine ka iya assasa matsalar man fetur a Najeriya, saboda yadda za a iya tsaida abubuwan da ake samarwa daga man daga ?angaren matatar.
Kamfanin NNPC ya bayyana cewa, a halin yanzu, an dakatar da shigowa da abubuwan da ake samarwa daga man fetur cikin Najeriya. “Za mu iya siffanta abunda muke fuskanta a halin yanzu a matsayin annoba, wanda ke aukuwa idan abubuwa da dama basu tafiya yadda ya kamata a lokaci daya.
“Muna fuskantar matsaloli, amma wannan matsalar tana faruwa ne a lokacin da wata matsalar ta faru, hakan yasa komai ya hargitse”
Rasha kasa ce dake samar da man fetur, ita kuma Ukraine ke tace mana kayan da aka tato daga mai a fadin duniya, ba gabashin Europe kadai ba. “Hakan yasa farashi ya daga, saboda tatattun kayayyakin suna zuwa ne daga wannan sassan duniya, kuma tashin hankali irin wannan zai zamo tangarda ga samar da kayyakin.”
“A kullum OPEC tana neman gangunan mai 1.7 miliyan daga Najeriya, amma abinda take iya samar wa yana tsakanin 1.3 zuwa 1.4 miliyan na gangunan man fetur a kullum.
Yanzu daga 1.3 miliyan na gangunan man da kasar ke samar wa a kullum, mutane na sata daga shi. “Su na yin ramuka a jikin magudanar man, inda ake amfani da man da suka sata a matatun da ba a yarda dasu ba a jihar Rivers, hakan ke sanya cuta da matsalar huhun mutane. Sauran wadanda suka sace, suna sawa a ababen hawa don siyarwa a manyan kasashe” .
