Yakar Yunwa: Bankin Duniya Zai Ba Afirka Tallafin Dala Biliyan Biyu

Rahotannin dake shigo mana daga birnin Washington DC na ?asar Amurka na bayyana cewar Bankin Duniya ya amince da tallafin ku?i na sama da dala biliyan biyu ga ?asashen Gabashi da Kudancin Afirka, don taimaka musu wajen bun?asa wadatar abinci.

A cikin wata sanarwa da bankin ya fitar, ya ce kimanin mutum miliyan 68 a yankin ke fuskantar matsalar ?arancin abinci da barazanar yunwa.

Ya ?ara da cewa matsalolin sauyin yanayi da tabarbarewar tattalin arziki da siyasa da rikice-rikice na kara ?amari.

Ya?in Ukraine ya ?ara haifar da matsalar ?arancin abinci a fadin duniya.

Bankin Duniya ya bayyana Habasha da Madagascar da suka da?e suna fama da fari, a matsayin kasashen da za su karbi kason farko na tallafin.

Related posts

Leave a Comment