Shugaban ?asa Muhammadu Buhari ya ce abin da ya sa bai cire tallafin man fetur ba shi ne don gudun tsananta wa al’ummar ?asar.
Shugaban ya fadi hakan ne a wata hira ta musamman da ya yi da jaridar Bloomberg ta intanet ta Amurka da aka wallafa a ranar Talata.
Bloomberg ta tambayi Buhari cewa me ya sa ya ?i amsa kiraye-kirayen da Asusun ba da lamuni na duniya IMF, da Babban Bankin Duniya ke masa tsawon shekaru na ya janye tallafin fetur kuma canjin ku?a?en ?asashen waje su zama na bai ?aya?
Sai ya amsa da cewa har yanzu akwai ?asashen yammacin duniya da ke bin tsarin biyan tallafin fetur.
“To me ya sa za mu janye namu a yanzu?
“Abin da ?asashen waje ke fama da shi shi ne sun fi mayar da hankali kan tsare-tsaren da aka yi a rubuce amma suna mantawa da tasirin haka ga al’ummominsu,” in ji shi.
A bara ne gwamnatin Shugaba Buhari ta so janye tallafin mai, “amma bayan tuntu?ar masu ruwa da tsaki da yadda abubuwa suka kasance a bana, ?aukar matakin ba mai yiwuwa ba ne.
Sai dai ya ce ?ara samar da albarkatun fetur a cikin ?asar ta hanyar sababbin matatun mai da ake sa ran za su fara aiki nan gaba a wannan shekarar za su taimaka sosai.
Kan batun tsadar ku?a?en ?asashen waje da mayar da farashinsu na bai ?aya kuma shugaban Najeriyar ya ce hakan na faruwa ne sakamakon wasu abubuwa da ke faruwa a wajen kasar.
“Idan aka ci gaba da samar da mai a cikin gida da tsare-tsaren samar da abinci, za a samu a daidaita farashin ku?a?en da mayar da su bai
