NDLEA Na Taimakon Dillalan Muggan Kwayoyi – Kyari

Labarin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar dakataccen Mataimakin Kwamishinan ‘Yan Sanda Abba Kyari, ya zargi jami’an NDLEA da ha?a baki da dillalan muggan kwayoyi ana safarar ?wayoyin cikin Najeriya.

Abba Kyari wanda NDLEA ta gurfanar a kotu bisa zargin hannun sa cikin safarar hodar ibilis, ya ce jami’an NDLEA sun gina masa rami ne ya fa?a, su ka yi masa sharrin cewa ya na mu’amala da hodar ibilis.

Babban laifin Abba a wurin NDLEA, a cewar sa, don kawai ya nemi hukumar ta biya wani ?an kwarmato ha??in sa, bayan ya taimaki Jami’an Tsaron ?aukin Gaggawa sun kama wani da ake zargi na safarar muggan ?wayoyi.

Cikin wata takarda da Abba Kyari ya dam?a wa kotu ya bayyana cewa shi ?anin Kyari ne, ya shaida wa kotun cewa NDLEA na ha?a baki da masu safarar ?waya, ita ce yadda idan sun shigo da ita, ake barin su wuce ba tare da an yi masa bincike ba.

Related posts

Leave a Comment