Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Shugaban ?asa Muhammadu Buhari zai halarci taron shugabannin ?ungiyar Commonwealth na ?asashe rainon Ingila da ke gudana a ?asar Rwanda daga 20 zuwa 26 ga watan Yuni.
Wata sanarwa da fadar shugaban ?asa ta fitar a ranar Laraba ta ce shugaban zai halarci bu?e bikin a hukumance ranar Juma’a.
Taron mai la?abin CHOGM 2022, zai tattauna kan halin rayuwa da kuma ci gaban al’ummar ?ungiyar fiye da biliyan biyu da ke zaune a ?asa 54 na nahiyoyin Afirka da Asiya da Amurka da Turai da kuma yankin Pacific.
