Wahala Da Tsadar Rayuwa Sun Karu A Tarayyar Najeriya – Hukumar Kididdiga

Labarin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Hukumar Kididdiga ta ?asa ta ce an samu ?aruwar hauhawar farashin kayayyaki a watan Janairun 2023.

Hukumar ta ce ta sanar a ranar Laraba cewa hauhawar farashin kayayyakin ya haura zuwa kashi 21.82 cikin ?ari idan aka kwatanta da kashi 21.34 cikin dari a watan Disamba.

Rahoton ya yi nuni da cewa hauhawar farashin kaya a shekara ya kai kashi 6.22 bisa ?ari idan aka kwatanta da na watan Janairun 2022, wanda ya kai kashi 15.60.

Rahoton ya ce kayayyakin da farashinsu ya tashi sun ha?a da burodi wanda ya kai kashi 21.67 da dankali da dawa, da doya da kuma na kayan lambu.

Bugu da ?ari, rahoton ya bayyana cewa farashin kayayyakni a cikin Janairu 2023 yana kashi 1.87 a kowane wata.

Haka na zuwa ne yayin da ‘yan ?asar ke ci gaba da fuskantar matsalar ?arancin sabbin takardun ku?i sakamakon sake fasalin ku?i da gwamnati ta yi.

Matsalar ta jefa ‘yan ?asar da dama cikin wahalhalu, inda suke fuskantar kalubale wajen biyan bukatun yau da kullum.

Kungiyar Gwamnonin Najeriya ta yi garga?in cewa wannan manufar na iya jefa tattalin arzikin ?asar cikin wani mawuyacin hali.

Related posts

Leave a Comment