Sau Miliyan 13 Muna Dakile Kutse Ta Internet A Zaben Shugaban Kasa – Hukumar Sadarwa

Rahoton dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Hukumomi sun bayyana cewar ?asar ta da?ile yun?urin kutse ko hare-hare a kan hanyoyin sadarwa na intanet har kimanin miliyan 13 a lokacin za?en shugaban ?asa da aka gudanar.

Babban daraktan hukumar bun?asa fasahar sadarwa ta Najeriya, wato NITDA, Kashifu Inuwa AbdulLahi, shi ya bayyana haka a lokacin da yake tattaunawa da BBC, inda ya ce an samu nasarar ce sakamakon wasu cibiyoyi da aka kafa don ya?i da kutsen ta intanet da kuma wani kwamiti na musamman da aka kafa da ya ?unshi hukumomin NITDA da NCC da Galaxy Backbone.

Ya ce a ranar za?e ka?ai sun da?ile yun?urin kutse har miliyan shida da dubu ?ari tara.

Daraktan na NITDA ya ce an yi ?o?arin yin kutsen daga cikin gida da kuma ?asashen waje saboda suna amfani da wasu manhajoji.

Ya ce kutsen ya shafi shafukan intanet na hukumomi da na kamfanoni masu zaman kansu da kuma na hukumar za?e wanda shi ne aka fi kai wa hari saboda za?e.

Ya ce babban hatsari da ke tattare da yin kutsen, shi ne hakan zai sa a de?i bayanai da canza wasu da kuma sanya wa mutane shakku kan amincewa da sahihan bayanai.

Related posts

Leave a Comment