Gwamnatin Tarayya Ta Dage Gudanar Da Aikin Kidaya

Rahoton dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana gwamnatin tarayya ta ?age aikin ?idayar jama’a da ta shirya fara gudanarwa ranar 29 ga watan Maris zuwa watan Mayu mai zuwa.

Ministan ya?a labaran ?asar Lai Mohammed ne ya bayyana haka ga manema labarai jim ka?an bayan kammala taron majalisar zartarwar ?asar da shugaban ?asar Muhammadu Buhari ya jagronta a Abuja fadar gwamnatin ?asar.

Lai Mohammed ya ce matakin ?age aikin ?idayar ya zama wajibi ne bayan da hukumar za?en ?asar ta ?age za?ukan gwamnoni zuwa ranar 18 ga watan Maris, a maimakon ranar 11 ga watan kamar yadda aka tsara gudanar da shi a baya.

Related posts

Leave a Comment