Labarin dake shigo mana daga Jihar Bauchi na bayyana cewar wata Kotu ta tsare fitaccen Malamin addinin Musulunci na Bauchi kuma babban limamin Masallacin Jumu’a Dutsen Tanshi, Dakta Idris Abdulaziz, a gidan gyaran hali.
An ruwaito cewa an tsare Malamin a gidan Yari ne bisa zargin yana amfani da wasu kalamai a karatuttukansa da ka iya tunzura jama’a.
Da yake tabbatar da haka, Lauyan Malamin, Barista Umar Hassan, ya ce rundunar yan sandan Bauchi ce ta gurfanar da Dakta Idris a gaban Kotun Majistire ranar Litinin.
Alkalin Kotun ya ?i aminta da bukatar Beli, inda ya umarci a tafi da Malamin zuwa gidan gyaran hali kuma idan Allah ya kaimu yau talata a dawo da shi gaban Kotu.
A wani wa’azi da ya yi a cikin watan Ramadan, Sheikh Idris ya fa?i wasu kalamai da suka haddasa cece kuce da muhawara mai zafi tsakanin mabiya addinin Musulunci.
Wasu daga cikin Malaman Musulunci sun fassara Kalaman Sheikh Idris da miyagun kalaman batanci ga fiyayyen halinta, Annabi Muhammad (SAW). Wasu Malami sun bu?aci mahukunta su gaggauta kama shi kan wa?annan kalamai da ya yi yayin da wani sashin malaman kuma suka goya masa baya.
Idan baku manta ba, a wancan lokacin hukumar kula da harkokin shari’ar Musulunci a Bauchi ta shirya zaman titsiye Malamin amma daga baya ta ?aga saboda wasu dalilai.
