Wasu ‘ya’yan Jam’iyyar APC a Karamar Hukumar Jalingo ta Jihar Taraba sunce basu amince da sanarwar da Kwamitin Zaben tayi na aiyana sunan wani a matsayin Shugaban da yayi nasara ta hanyar zaben lumana wato ‘concensus’ a turance.
Mai magana da yawun Membobin Ahmed Muhammed Hamza ya tabbatarwa manema labarai haka a Birnin Jalingo, Fadar Jihar Taraba cikinsu harda Wakilin Liberty, Bashir Adamu.
Da yake jawabi cikin bacin rai a madadin sauran fusatattun Membobin Jam’iyyar ta APC a Karamar Hukumar Jalingo, Ahmed Muhammed Hamza ya ce tun Karfe 9 na safe har zuwa 2 na rana suna wurin zaben kamar yadda kwamitin Zaben ya umurce su dayi, amma basuga koda wakilin zabe daya ba, amma abun mamaki kwatsam sai sukaji wai an zaba musu Shugaba ta hanyar maslaha, wanda a cewarsu bazasu aminta da hakan ba.
Muhammed Hamza na mai cewa ‘ai Mutane Jam’iyya ba Aljanu ba, kuma mune Mutanen, saboda haka, myna shaida a shirye muke muyi duk abunda doka ya tanada domin ganin mun kwace yancin mu da wasu tsiraru suka tauye mana’.
Fusatattun membobin Jam’iyyar sun kirayi jagorancin Uwar Jam’iyyar ta APC na Kasa da suki amincewa da duk wani rahoto da Kwamitin zasu kawo musu, domin a cewarsu bada amincewar mafi yawancin Membobin Jam’iyyar ta Karamar Hukumar Jalingo bane, kuma su gaggauta turo wani Kwamitin da zai gudanar musu da sahihin zaben Shugabansu.
Ahmed Muhamned Hamza ya roki magoya bayansu da suyi hakuri sukai hankali nesa domin sunada yakinin Uwar Jam’iyyar APC ta Kasa zasu amsa koken nasu da idon basira.
Duk kokarin da nayi domin jin ta bakin Kwamitin Zaben na Karamar Hukumar Jalingo yaci tura.
