Mun Kori Masu Tsattsauran Ra’ayin Addini Sama Da 600 Daga Kasarmu – Faransa

Ma’aikatar harkokin cikin gida ta Faransa ta kare matakin da ta ?auka na korar masu tsattsauran ra’ayin Islama daga ?asar, bayan wata ?ar takarar shugaban kasa ta ce za ta ?ara tsaurara matakai idan ta ci za?e.

Karamar ministaMarlene Schiappa ta ce sama da mutane 600 da ake zargi masu tsattsauran ra’ayi ne aka tasa keyarsu daga ?asar tun a 2018.

Yar takarar shugaban ?asa mai ra’ayin mazan jiya, Valerie Pecresse, ta fa?awa wata jaridar da ke fitowa duk Lahadi cewa idan aka zabe ta a shekara mai zuwa za ta bun?asa yaki da ta’addanci ta hanyar farfa?o da laifukan ya?i da suka shafi musayar bayanai da abokan gaba.

Ta ce duk shekara za ta kori mutane kusan 1500.

A ranar Laraba, mutane 20 ne za su gurfana a gaban kotun Paris da ake tuhuma suna da ala?a da hare-haren da aka kai a gidan rawa da filin wasan kwallon kafa da mashaya da gidajen cin abinci wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane 130 a watan Nuwamban 2015.

Related posts

Leave a Comment