Shugabancin Kasa: Tinubu Ne Mafita A Najeriya – Buhari

Rahotannin dake shigo mana daga jihar Sokoto na bayyana cewar Shugaban ?asa, Muhammadu Buhari, ya fa?a wa mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar III, cewa ya shiga ya?in neman zaben Bola Tinubu ne saboda abu uku.

Buhari ya bayyana haka ne yayin da ya jagoranci tawagar kamfen ?in shugaban kasa na APC zuwa fadar Sarkin Musulmi da ke Sakkwato domin neman tabarruki.

Shugaban ?asa ya ce tawagar yakin neman zaben ta ziyarci fadar Basaraken ne domin neman goyon bayan Sultan kuma ya zabi shiga cikin kamfen ne bisa dalilai uku.

A jawabinsa, shuga?an kasan ya ce shi da Bola Tinubu sun jima tare da juna a matsayin abokai tsawon shekaru 20, sannan abu na biyu ya yi abun a yaba lokacin yana gwamnan Legas.

“Dalili na uku shi ne Tinubu ya lashe tikitin takarar shugaban ?asa na APC a sahihi kuma ingantaccen za?e, bisa haka ya zama halastaccen ?an takara a jam’iyyata.” Daga nan kuma ya bukaci mai Alfarma Sarkin Musulmi da ya goyi bayan Tinubu, wanda Sultan da kansa ya kira da, “Jagaban duniya.”

“Na zo nan ne na roki ka marawa dan takararmu baya kuma na san cewa zaka ci gaba da goyon bayanmu,” inji Buhari.

Tun da fari, mai neman zama shugaban ?asa a inuwar APC, Bola Tinubu, ya fa?a wa Sarkin Musulmai cewa ya shiga tseren kujera lamba ?aya ne domin ya ci nasara.

“Babbar daraja ce zuwa nan musamman tare da rakiyar mai girma shugaban ?asa muka kawo ziyara fada. Kun riga kun sani amma bari na maimaita, mun zo nan ne domin a gabatar ni a matsayin ?an takarar APC.” “Mun san cewa baka tsoma baki a siyasa amma dole mu girmamaka idan muka shigo garin na yin kamfe.”

Related posts

Leave a Comment