Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar mai tsawatarwa a majalisar dattawa Sanata Uzor Kalu, ya bayyana cewa da kamar wuya jam’iyyar APC ta lashe zaben shugaban kasa idan bata dauki mataimaki Musulmi daga Arewa ba.
Ya bayyana hakan ne ranar Laraba yayin da yake hira da manema labarai a majalisar dokokin tarayya Abuja.
“Idan bamu dauki Musulmi mataimaki ba, mun shiga uku.” “Da kamar wuya mu lashe zabe saboda abu zabi daya da Ahmed Tinubu ke da shi shine kawai ya dauki Musulmi.”
“Mun shiga wani hali da ba zamu iya zaben marasa rinjaye biyu ba- Tinubu Musulmi ne daga kudu idan Kirista ke da rinjaye, sannan kuma daukan Kirista mara rinjaye daga Arewa shine mafi hatsari wannan shine gaskiyar lamari.” “Amma fa wannan ra’ayina ne.”
