Gwamna Darius Ishaku na Jihar Taraba ya roki ‘yan Najeriya mazauna jihar wa?anda ya yi wa ba daidai ba a zamanin mulkinsa na tsawon shekaru Takwas, su yafe masa. Ishaku ya nemi afuwa ne a wurin taron Addu’o’i wanda ?ungiyar ?iristoci (CAN) reshen jihar Taraba ta shirya masa a Sakatariyar CAN da ke Jalingo.
Gwamnan ya ce ya yi farin cikin ganin yadda takensa, “Ku aminta da ni, zam kawo muku ci gaba,” ya ginu ya kafa jojiyoyi a zu?atan mutanen jihar Taraba, inda ya roki mazauna Jihar Taraba su aminta da tubalin zaman lafiya, soyayya da yafiya su jagoranci mu’amalarsu da sauran abokan zamansu.
Haka nan tun kafin wannan, a wurin taron addu”o’in godiya na musamman lokacin bikin Ista a Cocin Anglican da ke Mayo Dasa, Gwamna Ishaku ya du?a kan guyawunsa ya baiwa talakawa ha?uri. Gwamnan ya du?a har ?asa a gaban dandazon taron Jama’a ya nemi su yafe masa kura-kuran da ya yi musu a lokacin zangon mulkinsa na tsawon shekaru takwas.
