Ka Gyara Barnar INEC Kafin Mu Yafe Maka – Kungiyar Arewa Ga Buhari

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Zauren Middle Belt Forun (MBF) da yake martani ga batun Buhari, ya ce ‘yan Najeriya za su yafe masa ne kadai idan ya yi gyara kafin tafiyarsa.

A cewar zauren, abu daya da zai faru ‘yan Najeriya su yafe ma Buhari ba komai bane face ya gyara kuskuren da hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ta yi a zaben bana.

Zauren ya ce, ya lura INEC ta yi kuskure a zaben bana, don haka Buharin ya gyara don samun yafiyar ‘yan kasa, kamar yadda jaridar Daily Sun ta ruwaito.

“Idan yana son mu yafe masa, ya gyara kuskuren da hukumar zabe ta INEC ta yi ta yadda za mu samu wanda ya dace a ofishi kuma mu samu irin Najeriyar da muke nema. “Bai kamata ya mika mulki ga marasa gaskiya ba amma ya tabbatar mutumin da ya dace ya maye kujerar ofishin.”

Related posts

Leave a Comment