Labarin dake shigo mana daga birnin Maiduguri na jihar Borno na bayyana cewa wasu daga cikin tubabbun yan ta’addan Boko Haram sun saka riguna dauke da rubutu da ke cewa ‘Don Allah ku yafe mana’, ‘Mun tuba’, ‘Mu taru mu sake gina Borno’.
Da ya ke magana kan atisayen, Mala Mustafa, wani babban mai bincike a CDD, ya ce an yi atisayen don shirya mayar da su cikin mutane. “Hikimar atisayen shine CDD ta tallafawa gwamnatin Jihar Borno a matsayin wani aiki na shirya mayar da tsaffin mayakan cikin al’umma,” in ji Mustafa.
“Muna ganin akwai bukatar samu canji, musamman irin kyamatarsu da ake yi a cikin gari. “Muna son gina alaka mai kyau da amintaka tsakanin wadanda suka mika wuya da mutanen gari.”
Mustapha ya cigaba da cewa za a fadada atisayen zuwa wasu zababbun unguwanni a Maiduguri da garuruwa da ke makwabtaka da su, domin kai wa ga nasarar da ake nema.
A bangarensa, Abdullahi Ishaq, mashawarci na musamman ga gwamnatin Borno kan tsaro ya yaba da atisayen da CDD ta yi. “CDD ta samar da kayayyaki yin wannan aikin kuma suna taimaka mana da shawarwari a matsayinsu na abokan hulda,” in ji Ishaq.
Ya ce shirin da gwamnatin ta fara na tsawon shekara ya saka yan ta’adda da dama sun ajiye makamai, kuma ya taimaka wurin aikin dawo da zaman lafiya a Borno. Ya yi kira ga sauran yan Najeriya da kungiyoyi su taimaka wurin cigaba da atisayen, wanda ya ce na bukatar kudi da wasu nau’in tallafin.
