Alkalin Alkalan Jihar Kwara Ya Kwanta Dama

Rahoton dake shigo mana daga Ilori babban birnin Jihar Kwara na bayyana cewar Mai shari’a Sikiru Adeyinka Oyinloye na babbar Kotun jihar ya riga mu gidan gaskiya, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Marigayi Al?alin ya rasu ne ranar Lahadi, 23 ga watan Afrilu, 2023 bayan kwashe dogon lokaci yana fama da ciwon da ya shafi wuyansa.

Wata majiya ta bayyana cewa Al?alin ya taba zuwa ?asar Indiya neman magani, ya rasu yana da shekara 58 a duniya yana kan aikinsa. Marigayi Oyinloye, ?an asalin kauyen Ijara Isin ne da ke karar hukumar Isin a jihar Kwara. Ya yi aiki a Babalakin & Co. gabanin na?a shi Al?alin babbar kotun jihar Kwara.

Kafin rasuwarsa, mai shari’a Oyinloye, Alkali ne da ake matu?ar ganin girmansa wanda ya yi kaurin suna wajen ‘Ba sani ba sabo’ a harkokin shari’arsa kuma yana da kirki. Ya kama mutane da dama da laifin halasta ku?in haram bayan hukumar EFCC ta gurfanar da su a gaban Kotu, inda ya umarci a kwace kadarorin da suka yi sama da fa?i da su.

A shekarar 2017, Marigayi Alkalin ya maka tarar biliyan N4bn kan jaridar Sahara Reporters da shugabanta, Omoyele Sowore, sakamakon wasu jerin labarai da suka wallafa kan tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki.

Related posts

Leave a Comment