Tallafin Mai: Mun Kashe Triliyan Biyu Cikin Wata Shida – Gwamnatin Tarayya

Gwamnatin Tarayya ta kashe naira tiriliyan biyu wajen biyan ku?in tallafin man fetur cikin wata shida na shekarar 2022, a cewar rahoton kamfanin mai na ?asar NNPC.

Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito cewa a ranar Talata ne NNPC ya gabatar da rahoton ga kwamatin asusun kasafi na ?asa wato Federation Accounts Allocation Committee (FAAC).

Saboda ?arin yawan ku?in da ake biya na tallafin ya sa NNPC bai bai wa gwamnatin ?asar ko kwandala ba a matsayin riba cikin shekarar nan, a cewar rahoton.

A shekarar da ta wuce, gwamnati na biyan naira biliyan 100 ne duk wata a matsayin ku?in tallafi. Shugabannin kamfanin ba su ce komai ba lokacin da Reuters ya nemi ?arin bayani.

A watan Janairu ne ya kamata ?asar ta dakatar da biyan tallafi amma sai gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta ?age matakin, tana mai cewa nauyin zai yi wa ‘yan ?asa yawa yayin da ake fama da hauhawar farashi.

Related posts

Leave a Comment