A karon farko, Saudiyya ta na?a wasu mata biyu a manyan mukamai na hukumar kula da masallatan Harami na Makka da Madina.
Gidan talabijin na Al Arabiya wanda mallakin Saudiyya ne, ya bayar da rahoto ranar Litinin cewa Sheikh shugaban hukumar Abdulrahman Al-Sudais ya na?a Dr. Al-Anoud Al-Aboud da Dr. Fatima Al-Rashoud a matsayin mataimakansa.
Al Arabiya ta ce hukumar na da niyyar horar da ma’aikata mata ’yan saudiyya 320, bayan sanar da fara shirin horon mai taken “Hayyak” a ranar 8 ga watan Agusta domin ha?aka ayyukan matan a masallatan masu tsarki.
Makamanciyar haka ta faru a shekarar da ta gabata, lokacin da ma’aikatar shari’a ta ?asar ta na?a mata 100 a matsayin ma’aikatan shari’a.
Dr Hala al-Tuwaijri ce jagorar sabon mu?amin, wadda a shekarar da ta gabata a wani taro ta sanar cewa “gwamnati ta saka taimakon mata a gaba, inda take ?orawa a kan tsare-tsarenta na baya.
Yarima Mai Jiran Gado, Mohammed Bin Salman – wanda ake gani a matsayin shugaban Saudiyya – na jagorantar ?udirinsa na Muradin 2030, wanda ke zai bai wa mata damar taka muhimmiyar rawa wajen ha?aka tattalin arzikin ?asar.
