Tsohon gwamnan Kano kuma Sanata mai wakiltar Kano ta Tsakiya, Sanata Ibrahim Shekarau, ya ce ?angaren rinjaye (APC) a majalisar Dattawa ne ya soma gabatar da batun neman a tsige shugaban kasa, Muhammadu Buhari, muddin bai ?au matakin kawo ?arshen matsalolin tsaro ba.
Sanata Shekarau wanda mamba ne a kwamitin tsaro na majalisar dattawa ya shaida hakan ne a wata hira ta musamman da ya yi da BBC.
Sanatan ya ce a lokacin zaman da majalisar ta yi kan halin da Najeriya ke ciki na ta?ar?arewar tsaro an shafe sama da sa’a uku ana dambarwa, kowa na tsokaci da kawo nasa ra’ayi, har aka kai ga matsayin neman a tura takardar tsigewa zuwa ga shugaba, Muhammadu Buhari bayan ba shi wa’adi.
Wannan batu na tsige Buhari kan matsalar ta?ar?arewar tsaro ya jawo yamutsi a zauren majalisar dattawan sakamakon zazzafar muhawarar da ‘yan majalisar suka yi a tsakaninsu.
Malam Ibrahim Shekaru ya ce ba zai ambaci suna ba, amma dai mutum na farko da ya soma gabatar da wannan batu na neman tsige shugaba Buhari a majalisa ?an APC ne, haka zalika mutum na biyu da ya goyi-bayansa kafin sauran mutane shi ma ?an APCn ne.
Ya ce “Ba zan soma kama sunan kowa ba amma wallahi ina tabbatar ma ka cewa wanda ya soma tashi ya ce a rubutawa shugaban ?asa takardar tsigewa wallahi ?an APC ne, wanda ya goyi-bayansa ma wallahi ?an APC.
“Wannan zama ne na ?aki da zama ne na zauren majalisa da kowa ya shaida, har da ‘yan jarida. Ina son mutane su san cewa maganar kalmar a tsige shugaban ?asa daga wajen APC ta fito ba ?angaren masu hamayya ba, su suka fa?i abin su.”
