Labarin dake shigo mana daga Ilori babban birnin Jihar Kwara na bayyana cewa tsohon Gwamnan Jihar Kano Rabiu Musa Kwankwaso ya ja kunnen ’yan Majalisa da su bi a hankali kan yunkurin tsige Buhari da suke kokarin yi kan Matsalar tsaron Najeriya.
Kwankwaso wanda tsohon Ministan tsaro ne ya gargadi ’yan Majalisar cewa kokarin tsige Buhari abu ne da zai iya tada tarzoma a Najeriya. Tsohon Ministan, ya ce tabbas al’amarin tsaro a Najeriya ya lalace kuma ya kamata gwamnati ta zage dantse wajen ganin an kawo karshen matsalar.
Kwankwaso wanda ke takarar shugaban kasa a jam’iyyar New Nigeria Party NNPP ya bayyana haka ne a lokacin da ya ziyarci Gwamnan Jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, dan halartar taron bude ofishin jam’iyyar NNPP a birnin Ilorin.
