Jam’iyyar APC mai mulkin ta fada cikin sabon rudani bayan shugabanta, Sanata Abdullahi Adamu, ya bayyana cewa sun amince da shugaban majalisar dattawa Sanata Ahmad Lawan a matsayin dan takarar shugaban kasa.
Bayanai sun nuna cewa Sanata Adamu ya bayyana haka ne a wurin taron kwamitin gudanarwa na jam’iyyar ta APC a Abuja ranar Litinin din nan.
Rahotanni sun nuna cewa Sanata Abdullahi Adamu ya shaida wa kwamitin gudanarwa na jam’iyyar ta APC matsayarsu ne bayan ya gana da shugaban kasar Muhammadu Buhari.
Ya sanar da wannan mataki ne kwana guda kafin zaben fitar da gwani na dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar.
Sai dai jim kadan bayan hakan, gwamnonin Jihohin arewac karkashin jam’iyyar APC sun yi watsi da matsayar shugaban jam’iyyar tasu.
Daya daga cikin gwamnonin ya shaida wa BBC cewa suna nan a kan bakansu na mika mulki ga kudancin kasar a zaben 2023.
Da yake jawabi ga manema labarai a fadar Aso Villa bayan ganawa da Shugaba Muhammadu Buhari, shugaban kungiyar gwamnonin arewacin Najeriya Simon Lalong na Jihar Filato, ya ce Shugaba Buhari ya tabbatar musu cewa bai goyi bayan wani mutum ba cikin mutum 23 da ke son jam’iyyar ta tsayar da su takara.
Shi ma da yake jawabi, shugaban kungiyar gwamnonin APC kuma gwamnan Jihar Kebbi, Atiku Bagudu, ya ce sun dauki matakin goyon bayan dan takara daga kudancin kasar ne domin tabbatar da adalci da zaman lafiya a kasar.
“Mun yi duba game da daukacin al’amuran kasarmu kuma mun yi amannar cewa jam’iyyar APC da Shugaban kasa sun raba romon dimokuradiyya ga dukkan bangarorin kasar nan… Abin da muke bukata shi ne a bai wa wasu bangarorin kasar dama. Kuma hakan zai kawo zaman lafiya,” in ji shi.
Shugaban APC ya sanar da wannan mataki ne kwana biyu bayan gwamnoni 11 na arewaci karkashin jam’iyyar sun amince mulki ya koma kudancin kasar bayan mulkin Shugaba Buhari.
Wannan matakin nan nufin sauran masu neman takarar shugabancin Najeriya karkashin jam’iyyar ta APC ba su samu tubarrakin jam’iyyar tasu ba.
