Ban Ce A Kirkiro Ma’aikatar ‘Yan Bindiga Ba – Gumi


Fitaccen malamin addinin musulunci nan mazaunin garin Kaduna Sheikh Ahmad Gumi ya yi ?arin haske kan shawarar da ya bayar ta bu?atar a samar da ma’aikatar kula da harakokin makiyaya a Najeriya.

Yayin zantawa da manema labarai a wani bikin nuna al’adun Fulani a Abuja, Shehin Malamin ya ce wasu kafofin ya?a labarai sun sauya abin da ya fa?a yana mai ?aryata rahotannin da ke cewa ya ce “ya kamata gwamnati ta ?ir?iro ma’aikatar ‘yan Bindiga ?arayin daji.”

“Sun mayar da makiyaya a matsayin ?an fashin daji,” kamar yadda Malamin ya bayyana a wani bidiyo da kafar talabijin ta Channels ta wallafa a Twitter.

Ya ?ara da cewa kashi 99.9 na makiyaya masu son zaman lafiya ne, yana mai cewa wasu tsiraru ne kawai ke haifar da wannan tashin hankalin da ake fama da shi.

Tun da farko Sheikh Gumi ya ce ya kamata gwamnati ta ?ir?iro ma’aikatar kula da makiyaya kamar yadda ta samar da ma’aikatar kula da harakokin yankin Neja Delta.

Ya ce akwai bu?atar a tattauna da su kuma a yi masu wa’azi da wayar masu da kai – “Musulmin ?warai ba zai kashe ko raunata wani ba a Najeriya.”

Ya ce wasu Fulani makiyaya sun bi tunaninsu na cewa “an manta da su a yayin da duniya ke ci gaba.”

Related posts

Leave a Comment