Shugabancin Kasa: Ayyana Ahmad Lawan Ya Haifar Da Rudani A APC

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Jam’iyyar APC ta fada cikin rudani bayan shugabanta Abdullahi Adamu, ya bayyana cewa sun amince da Sanata Ahmad Lawan a matsayin dan takarar shugaban kasa.

Sanata Abdullahi Adamu ya bayyana haka ne a wurin taron kwamitin gudanarwa na jam’iyyar ta APC a Abuja ranar Litinin.

Rahotanni sun nuna cewa Shugaban ya shaida wa kwamitin gudanarwa na jam’iyyar matsayarsu ne bayan ya gana da shugaban Buhari.

Amma wasu ‘yan kwamitin gudanarwar sun ce ba da yawunsa shugaban APC ya dauki matakin ba.

Jim kadan bayan hakan, gwamnonin Jihohin arewaci karkashin jam’iyyar sun yi watsi da matsayar shugaban jam’iyyar tasu.

Related posts

Leave a Comment