Adamawa: An Damke Matar Da Ta Kona Al’aurar ‘Yar Kishiyarta

Raundunan yan sandan jahar Adamawa tana tsare da wata mata yar shekaru sha takwas da haifuwa bisa zarginta da cin zarafin yar kishiyarta mai shekaru biyar.

Rundunan ta baiyana hakane a wata sanarwa da ta fitar dauke da sanya hanun kakakin rundunan a jahar Adamawa D S P Suleiman Yahay Nguroje wanda kuma aka rabawa manema labarai a yola fadar gwamnatin jahar ta Adamawa.

Sanarwan ya cigaba da cewa matar mai suna Aisha Muhammed wanda take zaune a anguwar wuro patuje a cikin karamar hukumar Mubi ta kudu dake jahar Adamawa, an samu nasran kamatane biyo bayan rahoton da mahaifiyar yarinya mai suna Aisha Abdullahi tare wata lauya mai suna Barista Khadida Nasir suka kaiwa Jami an yan sanda, wanda hakan yasa Jami an yan sandan basuyi da wasaba wajen kama matan da ake zargi da aikata wannan aika aika.

Ita dai Aisha Muhammed ana zarginta ne da yin amfani da karfe mai zafi wajen yiwa yar kishiyarta mai shekaru biyar da haifuwa rauni hanyar sanya mata karfen a jikinta harma da gabanta wanda avewarta yarinyar tayi mata fitsari a kan gado,

Bincike ya nuna cewa lamarin ya farune bayan mahafin yarinyar ya saki mahaifiyarta wato Aisha Abdullahi inda aka barta a hanun kishiyar uwarta wanda kuma kishiyar uwar Aisha Muhammed ta aikatamata wannan lamari.

Kwashinan yan sandan jahar Adamawa CP Aliyu Adamu Alhaji ya yabawa kunhiyar lauyoyi mata tare Jami an sandan bisa wannan namijin kokari da sukeyi na gano masu aikata laifuka a tsa kanin al umma.

Domin ganin an kawo ga karshen irin wandanan matsalolin nema kwamiahinan yan sandan jahar ta Adamawa C P Aliyu Adamu ya samar da Jami ai na misamman domin kare hakkin yara baki daya.

Yanzu haka dai Aisha Muhammed tana hanun yan sanda domin cigaba da bincike.kuma da zaran an kammala binciken za a gabatar da ita ga kotu domin ta fuskanci shariya.

Related posts

Leave a Comment