Labarin dake shigo mana daga Jihar Sokoto na bayyana cewar Baban malamin Kirista na Jihar Bishop Mathew Kukah ya ce yana nan lafiya ?alau biyo bayan rahotannin da aka ya?a cewa an kai masa hari lokacin zanga-zangar da ta ?arke a Sokoto ranar Asabar.
Bishop Kukah ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da ya fitar yana mai musanta cewa an ?ona gidansa.
Sai dai Kukah ya ce wasu masu zanga-zangar sun kai wa ginin cocin Holy Family Catholic Cathedral hari tare da farfasa gilasai da kuma ?ona wata mota da ke ajiye.
Tuni gwamnatin jihar ta sanya dokar hana fita baki ?aya bayan arangamar da aka yi tsakanin ‘yan zanga-zanga da jami’an tsaro ta jikkata mutum biyu.
Masu zanga-zangar na neman a saki mutanen da ‘yan sanda suka kama ne kan zargin kisan matashiya Deborah Samuel da suka zarga da zagin Annabi Muhammadu (SAW) ranar Alhamis da ta wuce.
