Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar ?ungiyar Gwamnonin arewaci ta yi kira da a kwantar da hankali bayan kisan wata matashiya da aka zarga da yi wa Manzon Allah ?atanci a Jihar Sokoto.
Cikin wata sanarwa da kafofin ya?a labarai suka ruwaito, gwamnan Filato kuma Shugaban ?ungiyar Simon Lalong ya ce ?ungiyar tasu na cikin damuwa game da halin da ake ciki a Sokoto.
“Gwamnonin sun damu da abin da ke faruwa, wanda lamari ne da ya sa?a wa sashen shari’a wajen ?aukar mataki,” a cewar Lalong.
“Gwamnonin Arewa na kiran a zauna lafiya bayan rahotannin riki?ewar zanga-zangar lumana zuwa rikicin da ya sa aka saka dokar hana fita a birnin Sokoto.”
Kazalika, gwamnonin sun ce duk wani yun?uri na ?aukar doka a hannu – kan lamarin addini ko akasin haka – “zai iya tayar da ?arin rikici”.
