Rahoton dake shigo mana daga Jihar Kaduna na bayyana cewar ‘ya’yan jam’iyyar APC a jihar sun roki babban jagoran su na kasa, Asiwaju Bola Tinubu da ya zabi gwamnan jihar, Mallam Nasir El-Rufai a matsayin abokin takararsa a zaben shugaban kasa na 2023.
A makon da ya gabata ne Tinubu ya ziyarci Kaduna don zawarcin kuri’un wakilan APC 69 a jihar gabannin zaben fidda gwani na jam’iyyar dake tafe.
Tinubu ya shaidawa wakilan cewa yana da karfin gwiwar cewa shine zai zama shugaban kasa na gaba idan Muhammadu Buhari ya sauka a shekara mai zuwa.
“Wasu na takara, ban san ina suke zuwa ba amma ni Villa za ni.” Kan haka, gaba daya wakilan APC a Kaduna sun lamuncewa Tinubu, yayinda jam’iyyar reshen jihar suka roke shi da ya zabi El-Rufai a matsayin abokin takara.
Da yake magana a madadin wakilan Kaduna, dan majalisa mai wakiltan Sabon Gari, Garba Babawo, ya roki Tinubu da ya dauki El-Rufai a matsayin abokin takararsa.
“Muna da wata bukata a gare ka (Tinubu), yallabai. Abun da nake shirin fadi, ban fadawa gwamnanmu ba saboda na san idan na fada masa ba zai goyi bayan haka ba. Muna so ka dauki gwamnanmu a matsayin abokin takararka.
“Ba ma so ya koma wajen kasar da zama bayan zaben domin mun san shirinsa. Shirinsa shine barin kasar da komawa kasar waje da zama bayan kammala wa’adinsa a matsayin gwamna. Amma muna so ya yiwa kasar hidima a matsayin abokin takararka.”
