Siyasa: Sarkin Yakin Jonathan Ya Koma APC

Labarin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Godsday Peter Orubebe wanda ya taba rike Minista a gwamnatin Jonathan, ya shiga jam’iyyar APC mai mulki bayan ficewarsa daga PDP.

Rahoton PM News ya tabbatar da cewa Elder Godsday Peter Orubebe ya sauya-sheka ne bayan abin da ya kira rashin tanadin PDP na karbe mulki a shekarar za?e ta 2023.

Da yake yi wa ‘ya ‘yan APC na kasar Ijaw jawabi a ranar Juma’a, 1 ga watan Yuli 2022, ‘dan siyasar ya shaidawa Duniya ya yi rajisa da APC a jihar Delta domin sauya alkiblar siyasar jama’ar shi.

Peter Orubebe yana cewa zai yi wa APC kokari wajen ganin duka ‘yan takaranta biyar sun yi nasara a babban zaben da za ayi na shekarar 2023.

Orubebe ya ce sai inda karfinsa ya kare musamman domin tabbatar da ‘yan takara uku da jam’iyyar ta tsaida a karamar hukumar Burutu sun yi nasara. An ji tsohon Ministan na Neja-Delta yana cewa zai yi tanadin duk abin da ake bukata a ci zabe.

Related posts

Leave a Comment