2023: Da Yiwuwar Zulum Ya Zama Mataimakin Tinubu

Dan takarar shuagaban kasa a jam’iyyar mai mulki APC na zaben 2023, Asiwaju Bola Tinubu, zai bayyana Zulum ko Kashim Shettima a matsayin mataimakinsa nan da ‘yan kwanaki kadan kamar yadda binciken jaridar Saturday PUNCH ta rawaito.

Yayin da ya rage kusan kwanaki 12 jam’iyyun siyasa su mika sunayen ‘yan takararsu na shugaban kasa da mataimakan takararsu ga hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa, Tinubu ya mika sunayen yan siyasan guda biyun bayan dogo nazari da shawarwari.

A jawabin wani makusancin Tinubu, yace shi ma Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai yana cikin wadanda ake tunanin dauka amma a karshe aka yi watsi da shi, duk da cewa ya taka rawar wajen ganin Tinubu ya fito a matsayin dan takarar jam’iyyar.

Jaridar Sunday PUNCH ata ruwaito cewa Tinubu, wanda a halin yanzu yana kasar Faransa, kuma ana sa ran zai dawo kasar nan ba da jimawa ba, domin kammala batun fitar da abokin takara kafin cikar wa’adin, ya takaita bincikensa ne a jihohin Borno, Kano da kuma Kaduna, inda duk yan takarar musulmai ne.

Related posts

Leave a Comment