Labarin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Godsday Peter Orubebe wanda ya taba rike Minista a gwamnatin Jonathan, ya shiga jamiyyar APC mai mulki bayan ficewarsa daga PDP.
Rahoton PM News ya tabbatar da cewa Elder Godsday Peter Orubebe ya sauya-sheka ne bayan abin da ya kira rashin tanadin PDP na karbe mulki a shekarar za?e ta 2023.
Da yake yi wa ya yan APC na kasar Ijaw jawabi a ranar Jumaa, 1 ga watan Yuli 2022, dan siyasar ya shaidawa Duniya ya yi rajisa da APC a jihar Delta domin sauya alkiblar siyasar jama’ar shi.
Peter Orubebe yana cewa zai yi wa APC kokari wajen ganin duka yan takaranta biyar sun yi nasara a babban zaben da za ayi na shekarar 2023.
Orubebe ya ce sai inda karfinsa ya kare musamman domin tabbatar da yan takara uku da jamiyyar ta tsaida a karamar hukumar Burutu sun yi nasara. An ji tsohon Ministan na Neja-Delta yana cewa zai yi tanadin duk abin da ake bukata a ci zabe.

