Shugabancin Kasa: Gwamna Bala Ya Raba Kafa

Labarin dake shigo mana daga Jihar Bauchi na bayyana cewar Gwamna Bala Mohammed ya sayi fam ?in sake yin takarar gwamna a ?ar?ashin jam’iyyar PDP, daidai lokacin da a gefe ?aya kuma ya ke neman takarar shugabancin Najeriya duk a cikin PDP.

Yayin da ya bayyana fitowar sa takarar shugaban ?asa a bayyane, Bala ya sayi fam na sake takarar gwamna a asirce.

Majiya ta shaida wa PREMIUM TIMES cewa bai tsaya a sayen fam ?in sake takarar gwamna ka?ai ba, tuni har ma an tantance shi, an amince ya kafsa da duk wanda ya fito takarar gwamna a za?en fidda gwani na PDP.

Bala dai na da ‘yancin sake tsayawa takara domin idan ya yi nasara, zai ?arasa zangon shekaru hu?u a Bauchi.

Dama dai an ra?e-ra?in cewa Sakataren Gwamnatin Bauchi Ibrahim Kashim ya ajiye aiki ya sayi fam ?in takarar gwamna ?ar?ashin PDP, bisa yarjejeniyar idan aka kayar da Bala a takarar shugaban ?asa, sai Kashim ya janye wa Bala ?in.

Related posts

Leave a Comment