Rahotannin dake shigo mana daga Jihar Kano na bayyana cewa Abdulmalik Tanko babban wanda ake zargi da kisan Hanifa Abubakar mai shekara biyar a Kano – ya musanta zargin kashe yarinyar.
Mutumin wanda ake zargi da sacewa tare da kashe Hanifa, ya musanta zargin da aka karanto masa shi da wasu mutum biyu a kotu yayin da ake ci gaba da shari’ar a yau Litinin.
Kazalika, Abdulmalik Tanko da Hashimu sun musanta zargin garkuwa da Hanifa da ba ta guba da kuma binne gawarta a wata makaranta kamar yadda aka ganu su a bidiyo suna amsawa tun da farko.
Sai dai sun amsa zargi ?aya cikin uku da aka karanto musu, wanda shi ne na ha?a baki.
Ita ma Fatima, wadda ke cikin wa?anda ake zargin, ta musanta zargin da aka karanto mata na rubuta wasi?a ga iyayen Hanifa cewa ana bu?atar ku?in fansa naira miliyan shida a madadin Abdulmalik Tanko.
Haka nan, Fatima ta musanta duka zarge-zargen da aka karanto mata.
A zaman da aka yi ranar 7 ga watan Fabarairu wa?anda ake zargin suka nemi gwamnati ta ba su lauyan da zai kare su. Barista M. L. Usman daga ?ungiyar Legal Aid da Barista P. A. Ademakun ke kare mutanen.
Lauyoyin gwamnati ?ar?ashin jagorancin Kwamishinan Shari’a Barista Musa Lawan sun nemi kotu ta ba su damar kawo shaidunsu a zama na gaba.
Mai Shari’a Sulaiman Naabba ya ?age zaman kotun zuwa 2 da 3 ga watan Maris mai zuwa don sauraron shaidu.
