Hajjin Bana: Muna Kokarin Rage Farashin Kujera – NAHCON

Shugaban Hukumar Hajji ta ?asa, NAHCON, Barista Zikrullah Kunle Hassan, ya baiyana cewa hukumar na nan na iya bakin ?o?arin ta na ganin cewa an rage farashin aikin Hajji na bana, duk da cewa ba makawa sai an ?ara farashin.

Kunle ya baiyana haka ne a sakon Sallah da ya fitar, wanda ya sanya hannu da kansa a yau Litinin.

A cewar sa, NAHCON na bin hanyoyin da su ka dace don ganin cewa an abu hanyoyin da su ka dace domin ganin cewa ?arin farashin aikin Hajjin bai yi yawan da har za a koka ba.

Sai dai kuma ya yi kira ga maniyyata da su ma su hanzarta su cika ku?a?en su kafin NAHCON ta sanar da farashin aikin Hajji da ta ?aiyade.

Ya ce biyan ku?in a kan lokaci zai baiwa hukumar samar sanin adadin alhazan Nijeriya, sai ta yi amfani da hakan wajen yin shirye-shiryen aikin Hajjin.

Hassan ya kuma bayyana sabbin tsare-tsare da a ka ?ullo da su a aikin Hajjin na bana.

Inda ya ?ara da cewa tuni NAHCON ta yi nisa wajen shirye-shirye na aikin Hajjin bana.

Related posts

Leave a Comment