Mata Na Baya A Samun Madafun Iko – Hukumar Kididdiga

 Wannan na ?unshe ne a wani rahoto da ya fito ranar Lahadi a Abuja daga Kundin ?ididdigar Jinsi na Watanni uku-uku, na wata ukun farko a 2022.

Kundin rahoton ya maida hankali ne a kan wasu lamura uku da su ka ha?a da, mulki, madafar iko, lafiya, ?ididdigar al’umma da kuma ilimi.

 A cewar rahoton, ?ididdiga ta nuna cewa kashi guda na mata da su ke fito wa a matsayin abokan takarar shugabancin ?asa da ga 2019 zuwa 2022 kashi 0 ne cikin 100,  yayin da na maza kuma 100 ne bisa 100.

 Rahoton ya ?ara da cewa adadin mata 6 ne su ka tsaya takarar shugaban ?asa a 2019, inda maza kuma 67 ne. Sai kuma ya kara da bayyana cewa adadin mata 26 ne su ka tsaya a matsayin abokan takara, a maimakon 52 daga ?angaren maza.

 Hakazalika, rahoton ya ce mata 80 ne su ka fito takararar gwamna a za?en 2019, inda maza kuma su  984 ne, inda mata 271 su ka zama abokan takarar gwamna, su kuma maza su 789 ne.

 Rahotan ya kuma yi nuni a ?angarori da dama da mu?aman maza su ka ninninka na mata a fa?in ?asar nan.

Related posts

Leave a Comment