An bayyana cewar babbar matsalar da Najeriya ke fuskanta a yanzu shine ta?ar?arewar shugabanci amma ba kwaskwarima ga kundin tsarin mulki ba, akwai gyara dangane da gyaran fuskar da ake yi wa kundin tsarin mulkin Najeriya a yanzu, abin da ke wakana shine tamkar an bar Jaki ne an koma dukan taiki gaba ?aya.
Tsohon dogarin Tsohon Shugaban kasa, Janar Sani Abacha, Watau Manjo Hamza Al-Mustapha ne ya bayyana hakan a yayin wata tattaunawa da aka yi dashi, ya bayyana cewa, garambawul din da akewa kundin tsarin mulkin Najeriya ba lallai ya kawo canjin da ake nema ba.
Hamza Al-Mustapha ya cigaba da cewar dalilin dake nuna hakan kuwa shine ana yin gyaran ne cikin gaggawa, wanda babu shakka bu?ata ba za ta biya a haka ba.
Ya bayyana hakane a ganawarsa da kamfanin dillancin labaran Najeriya, NAN inda ya kara da cewa, yawanci ana amfani da ra’ayin masu fada aji ne wanda kuma ba haka ya kamata ba.
Yace kamata yayi a ji ra’ayin mafi yawancin ‘yan Najeriya. Ya kara da cewa, mafi yawanci basu san ma da maganar gyaran kudin tsarin mulkin ba, wasu kuma basu ma da kudin da zasu fito daga kauyukansu su je wajen.
