Rahotanni daga Jihar Kano na bayyana cewar wasu matasa 17 daga jihar Kano sun gamu da ajalinsu a wani mummunan hatsarin mota da ya rutsa da su akan hanyar Zaria zuwa Kano ranar Asabar.
Hatsarin ya faru ne da yammacin ranar Asabar lokacin da matasan ke kan hanyar komawa Kano bayan sun halarci ?aura auren abokin su a Kaduna.
Matasan na cikin wata motar ‘Kano Line’ lokacin da hatsarin ya faru da su. Umar Abdullahi, abokin ?aya daga cikin mamatan, Umar Abba Sherrif, yace ya samu labarin mutuwar abokin nasa da misalin ?arfe 8:00 na dare.
Yace wacce ta fa?a masa mutuwar ta tabbatar masa da cewa abokin sa ya rasu ne nan take, Abdullahi yace takwas daga cikin matasan sun fito ne daga Sani Mainagge, ?aramar hukumar Gwale ta jihar Kano.
Goma sha daya daga cikin matasan sun rasu ne nan take yayin da sauran 6 suka ?arasa rasuwa bayan an kaisu asibiti.
Har yanzu ba’a gano musabbabin hatsarin ba, kuma an kira lambar kakakin hukumar kare ha?urra na jihar, Muhammad Kangiwa, amma wayarsa a kashe.
A ta’aziyyar da yayi wa iyalan mamatan, Gwamnan Abdullahi Ganduje, a wani jawabi da kakakinsa, Abba Anwar, ya fitar, gwamnan yace: “Wannan babban rashi ne mai ciwo ga iyalan matasan da kuma mutanen Sani Mainagge, ?aramar hukumar Gwale inda suka fito, sannan kuma damu baki ?aya, gwamnati da jama’ar jihar Kano.”
Ganduje yace wannan ?addara ce ta Allah, kuma shi ka?ai ne zai yafe musu, gwamnan yace: “Muna addu’a Allah SWT ya gafarta musu kurakuransu, yasa aljanna ce makomarsu, Su kuma iyalansu Allah ya basu hakurin jure wannan rashin da suka yi.”
