2023: Babu Abin Da Zai Hanani Takara – Atiku

Labarin dake shigo mana daga birnin Abeokuta na jihar Ogun na bayyana cewar tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar, ya jaddada aniyarsa ta tsayawa takarar shugabancin kasa a 2023, inda ya bayyana cewa tsofaffin yan siyasa ba za su hana matasan neman kujeran shugaban kasa a 2023 ba kamar yadda matasan ba za su hanna Dattawa nema ba.

Atiku ya bayyana hakan ne ranar Asabar a Abeokuta, jihar Ogun, bayan ganawa da tsohon shugaban kasa kuma tsohon maigidansa, Olusegun Obasanjo a ziyarar da ya kai masa.

Atiku ya ce nan ba da dadewa ba zai bayyana niyyar takararsa a zaben 2023. Hakazalika ya bayyana cewa yana da tabbacin nasara a zaben fidda gwanin jam’iyyar PDP.

“Shin na taba faduwa zaben fidda gwani ne? Ina da tabbacin samun gagarumar nasara akan abokanan takara ta”.

“Matasa suyi takara idan suna so. Takara ce. Demokradiyya ce.” Rahoton ya kara da cewa Atiku ya kai ziyarar ban girma wajen Sarkin kasar Egba, Oba Adedotun Gbadebo.

Related posts

Leave a Comment