An kira yi Gwamnatin tarayya da ta taimakawa masu sana ar P.O.S domin samun cigaban sana’ar tasu yadda ya kamata wanda sana’ar ta taimaka wajen samarwa matasa aikin yi a fadin Najeriya.
Shugaban Kungiyar masu sana’ar P.O.S a jihar Adamawa Auwal Usman ne yayi wannan kira a zantawarsa da wakilinmu a Yola.
Auwal Usman yace tun da gwamnati tana taimakawa sauran kungiyoyi to ya kamata suma a tuna da su kasancewar yawancinsu Matasa ne wadanda suke dogara da kansu.
Auwal ya kara da cewa sana’ar tasu tana fuskantar kalubale da dama saboda haka ya kamata gwamnatin tarayya ta dubesu da idon rahama da tallafa musu domin basu damar bunkasa harkokin nasu a fadin jihar dama kasa baki daya.
Usman ya kuma shawarci matasa da su kasance masu neman sana’ar dogaro da kai domin kare martabarsu a idon al’umma baki daya.
Har wayau ya kira yi shugabannin da su kasance masu kai dauki wa matasa a koda yaushe domin a cewarsa hakan zai taimaka wajen wanzar da zaman lafiya a tsakanin al’umma baki daya.
