Zan Cigaba Da Ayyukan Gina Al’umma Har Karshen Wa’adin Mulkina – Buhari

A ziyarar da mai girma Shugaban ?asa Muhammadu Buhari ya kai birnin Istanbul na kasar Turkiyya, Shugaba Buhari yayi bikin murnar cikarsa shekaru 79 a babban birnin Turkiyya ranar Juma’a.

Manyan hadimansa da Ministoci sun shirya masa bikin bazata karkashin jagorancin Ministan harkokin waje, Geoffrey Onyeama. Mamaki bisa abinda suka yi, Buhari ya yi alkawarin cewa ba zai daina yiwa Najeriya aiki da kokari ba har sai ranar da ya sauka daga karaga mulki.

Mai magana da yawun Shugaban, Malam Garba Shehu, ya bayyana hakan a jawabin da ya fitar ranar Asabar.

“Na yi tunanin tunda ba na Abuja zan tsira daga wannan abu. Ina sa ran komawa gona ta a gida idan na sauka a 2023.” “Amma kafin lokacin, zan cigaba da iyakan kokari wajen yiwa kasar nan da al’ummarta aiki kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada.”

A ziyarar Shugaba Muhammadu Buhari ya gana da Shugaban kasar Turkiyya, Recep Tayyip Erdogan, a safiyar ranar Juma’a, 17 ga Disamba, 2021 a birnin Istanbul.

Hadimin Shugaban Kasan, Buhari Sallau, ya bayyana hakan a hotunan da ya saki a shafinsa na Facebook. Shugabannin kasashen biyu sun yi zaman diflomasiyya tare Istanbul.

Related posts

Leave a Comment