Babu Gaskiya A Batun Tsige El-Rufa’i – Majalisar Dokokin Kaduna

Rahoton dake shigo mana daga jihar Kaduna na bayyana cewar Kakakin majalisar dokokin jihar Honorabul Yusuf Zailani, ya musanta duk wani shiri da ake ya?awa cewa ‘yan majalisar na yi da nufin tsige Gwamna Malam Nasiru El-Rufai.

Shugaban majalisar ya ayyana ra?e-ra?in tun?uke gwamnan kan tuhume-tuhumen da suka shafi cin hanci da rashawa a matsayin labarin ?arya mara tushe ballantana makama.

Rahoton shirin mambobin majalisa na tsige gwamna ya kara?e kafafen sada zumunta ranar Lahadi, 21 ga watan Agusta, 2022 lamarin da ya tayar da ?ura sosai a jihar da Najeriya gaba ?aya.

A wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Ibrahim ?ahiru ?anfulani, ya fitar, Zailani ya kuma ?aryata rahoton da ke cewa yanzu majalisar na gudanar da bincike kan kashe-kashen ku?in ma’aikatu da hukumomin gwamnatin jihar ta Kaduna.

“Hankalin shugaban majalisar dokokin Kaduna ya kai kan wani rahoto na shirin tsige Gwamna Malam Nasiru El-Rufai da ke yawo a kafafen sada zumunta.” “A saukake wannan aikin tsagin yan adawa ne da ma?iyan cigaba da ?asawa tsakanin ?angaren masu doka da majalisar zartaswa karkashin jagorancin Malam Nasiru El-Rufai.”

“Suna haka ne da nufin ta da yamutsi tsakanin ?angaren zartarwa da majalisa domin hana mutanen Kaduna cigaba da shan romom demokara?iyya da suke amfana da shi saboda kyakkywar ala?ar ?angarorin biyu.”

“Haka nan rahoton da ke ikirarin ala?ar gwamna da kakakin majalisa, Yusuf Zailani, ta yi tsami a yanzu ba komai bace illa shaci fa?i da gur?ataccen hangen mai rubutu da masu ?aukar nauyi.” “Saboda haka ina mai bayyana cewa baki ?aya jita-jitar shiryayyar ?eta ce da nufin gur?ata tunanin mutane kuma ya kamata kowa ya yi fatali da ita.”

Related posts

Leave a Comment