‘Yan Najeriya Ba Su Fahimci Fikihun Dakatar Da Tiwita Ba – APC

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Jam’iyyar APC mai mulki ta nuna damuwarta dangane da rashin fahimtar hikimar dake tattare da dakatar da shafin Tiwita da gwamnatin Buhari ta yi da ‘Ysn Najeriya ba su fahimta ba.

Shugaban Matasan na kasa na jam’iyyar APC, Ismaeel Ahmed, a ranar Laraba, ya ce Gwamnatin Tarayya ba ta hana amfani da Twitter ba, kawai ta dakatar da ayyukan sa ne.

Ya fadi haka ne a wani taron manema labarai da yake gabatarwa wanda aka sake tsarawa domin ci gaban taron matasa wanda zai gudana a mako mai zuwa a babban birnin tarayya Abuja.

Ahmed ya ce: “Gwamnati ba ta hana shafukan sada zumunta ba kamar yadda mutane da yawa za su yi zato. Yana da mahimmanci mu sani cewa Facebook har yanzu yana aiki, Instagram har yanzu yana aiki, WhatsApp yana aiki, kuma da yawa sauran dandamali na dandalin sada zumunta duk suna aiki.

“A zahiri, wasu mutane za su ce maka Twitter na fitattun matasa ne kuma ba lallai ne ya zama gama gari ba. “Ina ganin akwai masu yin Facebook da yawa a Najeriya fiye da Twitter.

Amma, har yanzu kafa ce mai mahimmanci ga mutane. “Don haka, duk abin da gwamnati ta yi na dakatar da Twitter, ba na hanawa ba, akwai dakatarwar, kuma ba shakka, akwai tattaunawa da ke gudana tsakanin gwamnati da wakilan Twitter kuma na tabbata za a warware matsalar.”

Ismaeel wanda jigo ne a APC ya kuma ce yayin da shi kansa ba ya farin ciki da dakatar da ayyukan shafin na yanar gizo, ba shi da wata matsala ta bayyana tarayyarsa da gwamnatin tarayya don daukar matakin.

‘Yan Najeriya da dama na kokawa kan dakatar da kafar sadarwar Twitter da gwamnatin Buhari tayi, lamarin ya jawo cece-kuce tsakanin fitattun ‘yan Najeriya wanda har gwamnati ta ce za ta hukunta duk wanda aka kama da hawa shafin na Twitter.

Related posts

Leave a Comment