Sana’ar Gyaran Takalmi Ta Yi Mini Komai – Bello Nasarawa

Muhammad Bello Adamu Nassarawa Dake Karamar Hukumar Chikun a Jihar Kaduna
Mai Sana’ar gyaran Takalmi ne Wanda ya shafe Sama Shekaru 35 Yana wannan Sana’ar yace Sana’ar Gyaran Takalmi wato Shoe Shiner Sana’a ce Mai cike da Rufin Asiri, domin a cikinta yake ci Kuma yake Sha harma da Sauran bukatunsa na yau da Kullum.

ya Kara da Cewa wannan sana’a tasa tayi Masa Riga da wando duk da Cewa wasu na Mata kallon sana’a ce ta Kaskanci amma agunsa ba haka abin yake ba.

Inda yace da Wannan Sana’ar yayi Aure Kuma ya Aurar duk da sana ar Kuma yanzun haka Yana da ‘Ya’ya da yake ciyar da su duk da Wannan Sana’ar ta Gyaran Takalmi.

Saidai yace Babban Kalubalen da Mafi yawan masu Sana’ar ke fuskanta shine Rashin Tallafin jari Mai kauri

Ya jaddada Cewa tun Daga lokacin da ya fara wannan Sana’ar har zuwa wannan lokaci Bai taba samun Tallafin ba Inda yace Inda Zai Samu jarin Dubu Dari ya ishe shi ya bunkasa Sana’ar ta yadda wasu ma da dama za su amfana Albarkacin wannan Tallafin idan ya samu.

Muhammad Bello yace ya shafe shekara biyu Yana koyon wannan Sana’ar Wajen Mai gidansa, Dukda kalubalen da ya fuskanta a lokacin Koyon Sana’ar Amma hakan Bai Kashe mashi Gwiwwa ba a wancen Lokacin.

Sannan ya bukaci matasa .na wannan zamani su rungumi Sana’ar Hannu Kuma suyi juriya Wajen koyon Sana’ar sannan su riketa da Muhimmancin gaske Inda yace hakan Zai hanasu shiga cikin Mummunan Hali Sakamakon Dogaro da kansu da suka yi.

Daga Karshe ya bukaci Gwamnatin Tarayya da ta Jihohin da Sauran Wadanda abin ya shafe Harma da Masu Hannu da Shuni su Rika Taimakawa matasa da Sauran masu Sana’ar Hannu domin hakan Zai Hana Matasan fadawa cikin ayyukan ta’addanci.

Yayi fatan Allah ya bamu Zaman Lafiya a Kasa Nijeriya da Kuma abinda Lafiyar za ta ci

Related posts

Leave a Comment