Ba Za Mu Amince Da Cigaba Da Zaman Sarkin Fulani A Oyo Ba – Yarbawa

Al’ummar Yarbawa Mazauna Garin Igangan da ke karamar hukumar Ibarapa ta Arewa a jihar Oyo sun dauki alkawarin cewa ba za su sake barin sarkin Fulani da aka kora a garin, Abdulkadri Saliu, ya sake dawowa ba har abada.

A cewarsu, barin shi ya sake dawowa garin daidai ya ke da kashe kansu da kansu, sun kara da cewa gara su mutu da su amince Saliu ya dawo garin.

“Gara dukkan garin su kashe kansu a maimakon su bari Sarkin Fulani ya dawo. Gara mu sadaukar da rayukan mu a maimakon mu bari jikokinmu da za su zo nan gaba su rayu karkashin mulkin zalinci na Sarkin Fulani,”.

Jagoran ?ungiyar masu neman cigaban Igangan, Oladiran Oladokun ya shaidawa jaridar The Punch. Oladokun ya yi wannan jawabin ne yayin da ya ke martani kan jawabin da Sarkin Fulani ya yi na cewa zai iya dawowa Igangan.

“Idan an bani dama komawa garin, zan iya komawa,” a cewar Saliu a ranar Alhamis, wadda iyalansa a halin yanzu sun yada zango a garin Ilorin na jihar Kwara.

Tun farko mun kawo muku rahoton cewa fitaccen mai kare hakkin Yarabawa, Sunday Adeyemo da aka fi sani da Sundau Igboho ya zargi makiyaya da aikata laifuka a kasar Ibarapa don haka ya basu wa’adin kwanaki bakwai su fice daga garin.

Bayan cikar wa’adin shi da yaransa da wasu mazauna Igangan sun fattaki Sarkin Fulani da wasu makiyaya daga garin ba tare da bata lokaci ba.

Related posts

Leave a Comment