Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar wata babbar kotun tarayya da ke birnin ta umurci gwamnan jihar Ebonyi, David Umahi ya sauka daga kan mukaminsa na gwamna ba tare da ?ata lokaci ba.
Kazalika kotun ta umurci mataimakin gwamnan da kakakin majalisar dokokin jihar da sauran ?an majalisar da suka sauya sheka tare da gwamnan daga jam’iyyar PDP zuwa APC su ma su Sauka daga mukamansu.
Kotun ta ce sauya shekar da suka yi daga jam`iyyar PDP zuwa APC ya saba wa kundin tsarin mulkin Najeriya, saboda haka ba su cancanci zama a kan kujerun nasu ba.
Harwayau, kotun ta bu?ace su da su mayar da baki dayan albashin da suka karba bayan sauya shekar tasu.
