Rahotanni daga Maiduguri babban birnin jihar Borno na bayyana cewar Gwamnan jihar, Farfesa Babagana Zulum, yace Magidanta yan gudun Hijira 500 daga Malam-Fatori, ?aramar hukumar Abadam, za su yi azumin Ramadan a gida idan Allah ya so.
Gwamnan ya yi wannan furucin ne yayin da ya kai wata ziyara yankin ranar Lahadi, kamar yadda gwamnatin Borno ta fitar a shafin Facebook.
Tun a farkon faruwar matsalar ayyukan ta’addancin ?ungiyar Boko Haram a shekarar 2014 mafi yawan mutanen garin Malam-Fatori suka bar gidajen su.
Yayin ziyarar da ya kai, gwamna Zulum ya duba gidajen wucin gadi 100 da magidantan ke amfani da su, kafin gwamnati ta kammala gyara musu gidajen su.
“Magidanta 500 da Izinin Allah za su dawo gida kafin watan Azumin Ramadana. Wannan ne lokacin da ya fi dacewa mu dawo da su gida cikin kwanciyar hankali kafin ruwa ya sauka.”
Gwamnan ya kuma ba da umarni ga ma’aikatar gyara da maida yan gudun hijira gida ta kammala ginin azuzuwa 5 na Firamare a yankin cikin kwanaki 10 masu zuwa.
Haka nan ya ba da umarnin a gyara Asibiti da kuma Masallacin Jumu’a dake kusa da tsohuwar kasuwar garin.
Gwamna Zulum ya ?ara da cewa kowane Magidanci da za’a dawo da shi gida, zai samu tallafin N100,000 a wani bangare na taimaka masa ya sake gina kansa.
