Sai Da Na Gargadi Obasanjo Kan Shiga Siyasa – Abdulsalami

Tsohon shugaban mulkin soji Janar Abdulsalami Abubakar ya bayyana yadda ya bai wa tsohon shugaba Olusegun Obasanjo shawarar kada ya shiga siyasa jim kadan bayan ya fito daga gidan yari.

An tsare Obasanjo ne lokacin shugabancin Janar Sani Abacha kuma ya fito bayan Abdlsalami ya zama shugaban kasa.

Bayan nan kuma Abdulsalami ya mika ragamar kasar ga Obasanjo bayan an zabe shi shugaba a 1999.

An ta sukar Abdulsalami kan mika kasar da ya yi ga wanda ya fito kai tsaye daga gidan yari.

A wata tattaunawa da ya yi da Trust TV Abdulsalami ya yi martani ga masu irin wannan tunani, inda yace wata rana Obasanjo ya ziyarce shi, ya kuma gaya masa mutane na son ya tsaya takara.

Abdulsalam ya ce ya ba shi shawara kan cewa ya yi watsi da wadannan kalamai na mutane ya tafi ya huta.

Related posts

Leave a Comment